Isa ga babban shafi
Afrika

An ki gayyatar Tutu bikin Jana’izar Mandela

Archbishop Desmond Tutu wanda ya karbi lambar yabo ta zaman lafiya zai kauracewa Jana’izar abokinsa Nelson Mandela saboda ba a gayyace shi ba bisa wasu dalilai na siyasa. A yau Assabar ne mutanen Afrika ta kudu ke yin bankwana da gawar Mandela kafin a binne shi a ranar Lahadi.

Archbishop Desmond Tutu yana yi wa Nesldon Mandela addu'a
Archbishop Desmond Tutu yana yi wa Nesldon Mandela addu'a REUTERS/Mark Wessels
Talla

‘Yar malamin na Kiristoci kasar Afrika ta kudu Mpho Tutu ta tabbatarwa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa ba a gayyaci mahaifinta ba.

Desmond Tutu yana cikin wadanda ke kalubalantar Jam’iyyar ANC mai mulki ta Jacob Zuma, amma Roger Friedman, mataimakinsa na musamman ya ki cewa komi akan dalilan da ya sa aka ki gayyatar Tutu.

A gidan Tutu ne Nelson Mandela ya fara sauka bayan an sako shi daga gidan yari inda ya kwashe tsawon shekaru 27 a kargame, kuma tun lokacin ne Mandela da Tutu suke tare da juna.

A yau Assabar ne mambobin Jam’iyyar ANC ke yin taron bankwana da gawar Nelson Mandela wanda aka shirya binne wa a gobe Lahadi.

Shugaba Jacob Zuma ne ke jagorantar manyan shugabannin Jam’iyyar a bikin da suka shirya na girmama Mandela wanda ya kafa Jam’iyyar.

Za’a binne Mandela ne a kauyen Qunu inda ya yi rayuwa a gabacin lardin Cape. Akalla mutane 100,000 ne suka kai wa gawar Mandela ziyarar girmamawa a Pretoria a tsawon kwanaki uku da suka gabata. A ranar 5 ga watan Disemba ne Mandela ya mutu yana da shekaru 95 a duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.