Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Mutanen Afrika ta Kudu suna kai wa gawar Mandela ziyarar girmamawa

Mutanen Afrika ta kudu sun yi jerin gwano domin kai wa Gawar Tsohon shugabansu Nelson Mandela ziyara ta karshe kafin a binne shi. Dubban mutane ne ke ci gaba da yin tururuwa inda suke zagaya akwatin gawar tsohon shugaban wanda aka ajiye domin yi masa karramawar karshe har na tsawon kwanaki uku.

Jerin Gwanon Mutanen Afrika da ke kokarin kai wa gawar Mandela ziyarar girmamawa a Pretoria
Jerin Gwanon Mutanen Afrika da ke kokarin kai wa gawar Mandela ziyarar girmamawa a Pretoria REUTERS/Kevin Coombs
Talla

Da dama daga cikin wadanda suka ziyarci inda aka ajiye akwatin gawar ta marigayi Mandela, sun bayyana cewa har abada ba za su taba mantawa da shi ba saboda rawar da ya taka domin samarwa al’ummar kasar ta Afirka ta Kudu ‘yanci.

A ranar Alhamis ne 5 ga watan Disemba Nelson Mandela ya rasu yana da shekaru 95 a duniya kuma a ranar Lahadi ne za’a binne shi a kauyen Qunu da ke gabacin lardin Cape.
Yanzu haka an ajiye gawar Mandela ne a ginin Fadar Gwamnatin Afrika ta Kudu wanda shi ne shugaban kasa bakar fata na farko a kasar.

“In ba don Mandela ba, da ba zamu samu damar kansacewa a wannan wuri ba, kuma ba dominsa ba, da ba mu shiga makarantu domin samun ilimi ba, ya je gidan yari ne saboda mu, wannan ne dalilin zuwa na wannan wuri a yau” a cewar wata ‘Yan kasar Afrika ta kudu da ta kai ziyara domin girmama gawar Mandela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.