Zambia
Kotun Zambia ta wanke Rupiah Banda daga zargin karbar cin hanci da rashawa
Kotu a kasar Zambia a yau ta wanke tsohon shugaban kasar Rupiah Banda, game da zargin da ake yi ma sa na karbar wasu motoci domin gudanar da yakin neman zabe.
Wallafawa ranar:
Talla
An zargi Banda da karbara motocin ne ba a kan ka’ida ba daga wani kamfanin gine-gine mallakin kasar China.
Banda dan kimanin shekaru 76 a duniya, ya mulki kasar Zambia daga shekarar 2008 zuwa 2011, kuma ana zargin cewa ya yi amfani da mukaminshi domin karbar motocin daga wannan kamfani kafin kotun ta wanke shi a yau.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu