Isa ga babban shafi
Najeriya

An sake katse wasu hanyoyin sadarwa a jahohin da ke cikin dokar ta baci a Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta sake haramta yin amfani da hanyoyin sadarwa ta hanyar tauraron Dan Adam a jahohin arewa maso gabacin kasar bayan katse wayoyin salula saboda ikirarin da Sojin suka yi cewar hanyoyin sadarwar suna taimakawa 'Yan Boko Haram wajen kai hare hare.

Allon sanawar da ke bayanin neman Abubakar Shekau shugaban  Boko Haram ruwa a jallo da kuma kudaden lada ga duk wanda ya taimaka aka kama shi
Allon sanawar da ke bayanin neman Abubakar Shekau shugaban Boko Haram ruwa a jallo da kuma kudaden lada ga duk wanda ya taimaka aka kama shi REUTERS/Tim Cocks
Talla

Wani hari da aka kai na bayan nan a makarantu ya kashe dalibai kimanin 16.

Sanarwar da ta fito daga Laftanal Kanal Sagir Musa, Sojin kasar sun ce daga ranar 19 ga watan Yuni sun haramta amfani da wayoyin Thuraya da makamancinsu a jahar Borno.

“Duk wanda aka kama yana amfani da wayar Thuraya, ko katin wayar za’a cafke shi” a cewar sanarwar.

Sai dai babu wani cikakken bayani ko wannan dokar ta shafi ‘Yan jarida wadanda ke amfani da hanyoyin tauraron Dan Adam domin gudanar da ayyukansu na yada abubuwan da ke faruwa a yankunan da aka kafa wa dokar ta baci.

A ranar Lahadi ne wasu ‘Yan bindiga da ake zargin ‘Yan Boko Haram ne suka bude wuta a wata makarantar Sakandare da ke garin Damaturu a Jahar Yobe, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar dalibai 7 da malaman makaratar guda biyu.

Haka ma, a garin Maiduguri wasu ‘Yan bindiga suka budewa wasu dalibai wuta guda Tara a lokacin da suke rubuta jarabawa.

Tuni dai kungiyoyin fararen hula da kungiyar Lauyoyi a Najeriya suka ce za su shigar da kara domin ganin an dage takunkumin amfani da wayoyin salula a jahohin da aka kafawa dokar ta baci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.