Isa ga babban shafi
Najeriya-Ghana

Matsalar tsaro a Najeriya barazana ce ga kasashen Afrika, inji shugaban Ghana

A lokacin da ya kawo ziyara kasar Faransa, Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama yace mastalar tsaro a Najeriya barazana ce ga kasar Ghana, yana mai bayyana fatar gwamnatin Najeriya za ta dauki matakan magance matsalar kafin ta shafi sauran kasashen da ke makwabtaka da ita.

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama a lokacin da yake zantawa da sashen Turanci na RFI
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama a lokacin da yake zantawa da sashen Turanci na RFI DR
Talla

“Matsalar tsaro barazana ce ga Ghana, domin Najeriya babbar kasar ce a yammacin Afrika ta fannoni da dama” a cewar shugaba Mahama.

Bayan ganawa da shugaba François Hollande, Mista Mahama ya jinjinawa gudunmuwar da Faransa ke ci gaba da bayar wa a rikicin arewacin Mali.

Shugaban na Ghana yace matsalar mayaka babbar barazana ce ga kasashen yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.