Isa ga babban shafi
Algeria-France

Ana tantance labarin rashin lafiyar Bouteflika na Algeria

Hukumomin kasar Algeria, sun fara tantance labarun wasu jaridun kasar biyu, sakamakon rahotannin da suka dauka, kan rashin lafiyar shugaban kasa Abdelaziz Bouteflika, da suka ce yana cikin halin mutu ko kai rai ko koi, makwanni uku bayan kwantar da shi a wani asibitin kasar Faransa.

Shugaban Algeria, Abdelaziz Bouteflika.
Shugaban Algeria, Abdelaziz Bouteflika. REUTERS/Louafi Larbi
Talla

Wannan matakin da hukumomin suka dauka ya sa aka fara rade radin halin da shugaban yake ciki.

Babban mai gabatar da kara na kasar, ya umarci a gurfanar da babban editan jaridar, Hichem Aboud, inda ake zargi da zagon kasa a lamuran tsaron kasar.

Mai gabatar da kara ya zargi Aboud da yada labain da ba shida tushe, inda ya ce an dawo da Bouteflika kasar ranar Larabar da ta gabata, amma bai san halin da yake ciki ba.

A shekara mai zuwa ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasar, kuma halin lafiyar shugaban ya tayar da muhawara mai zafi tsakanin jama’a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.