Isa ga babban shafi
Aljeriya

An kwantar da Abdoul Aziz Bouteflika a wani asibitin Faransa

Hukumomi a kasar Aljeriya, sun ce sakamakon matsalar bugun jinni da shugaban kasar ke fama da ita, yanzu haka an kwantar da Abdoul Aziz Boutheflika a wani asibitin sojoji da ke Val-de-Grâce na kasar Faransa domin jinya.

Shugaban Aljeriya, Abdelaziz Bouteflika.
Shugaban Aljeriya, Abdelaziz Bouteflika. AFP PHOTO Pool Denis Allard
Talla

Rahotanni sun ce da misalin karfe daya da rabi na ranar jiya asabar ne likitoci suka lura cewa jiyojin da aikewa da jinni zuwa sassan jikin shugaban kasar sun toshe, lamarin da ya sa aka dauki matakin gaggawar fitar da shi zuwa Faransa.
Shi dai Abddoul Aziz Boutflika dan kimanin shekaru 76 a duniya, ya dare kan karagar mulkin kasar Aljeriya ne tun a shekara ta 1999, kuma ya jima yana fama da wannan matsala ta bugun jinni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.