Isa ga babban shafi
Najeriya

Dokar hana fita dare da rana a unguwanni 12 na Maiduguri.

Rahotanni daga yankin arewa maso gabashin tarayyar Najeriya na cewa yanzu haka jama’a na ci gaba da tserewa daga yankin, sakamakon farmakin da sojan sama kasar ke kai wa wani wuri da ake zaton cewa maboyar ‘yan kungiyar Boko Haram ne.

Dakarun Najeriya
Dakarun Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A garin Kwalaram da kuma Gomborun Gala da ke cikin jihar Borno kusa da iyakar kasar da Jamhuriyar Kamaru, rahotanni sun ce daruruwan mutane ne suka gudu suka bar gidajensu daga lokacin da sojoji suka kadamar da wannan farmaki.
Wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Faransa cewa, wata rokar da mayakan kungiyar Boko Haram suka harba, ta yi wa daya daga cikin jiragen saman yakin sojan na Najeriya mummunan ta’adi, lamarin da ya tilasta wa jirgin yin saukar gaggawa.
Yanzu haka dai gwamnatin kasar ta sanar da kafa dokar ta baci a wasu jihohi uku da ta ce suna fuskantar matsalar tsaro, wato Borno, Yobe da kuma Adamawa.

A daya bangare kuwa, rundunar hadin gwiwa da aka kafa domin tabbatar da tsaro a jihar Borno wato JTF, ta sanar da kafa dokar hana fita dare da rana a wasu unguwanni 12 da ke birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar ta Borno.

Sanarwar kafa wannan doka, ta fito ne daga kakakin rundunar Laftanar Kanar Sagiru Musa, to amma dai babu wasu cikakkun bayanai a game da kafa dokar a daidai lokacin da jama'a ke rayuwa a cikin yanayi na dokar ta baci a jihar da kuma sauran jihohi biyu da ke yankin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.