Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Taron Tallafawa Rikicin kasar Mali a Addis Ababa

An bude taron tallafawa rikicin kasar Mali wanda ya kunshi shugabannin kasashen Afrika da wakilai daga Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da kuma Japan bayan Faransa ta kaddamar da yaki domin kwato yankin Arewaci da ya fada hannun ‘Yan tawaye.

Shugaban Mali  Dioncounda Traoré,  à Addis-Ababa.
Shugaban Mali Dioncounda Traoré, à Addis-Ababa. REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Karbe ikon Timbuktu na zuwa ne kwanaki 18 da Faransa ta kaddamar da yaki a Mali domin kwato yankin Arewaci da ‘Yan tawaye suka karbe watanni 10 a lokacin da Sojoji suka hambarar da gwamnatin Amadou Toumani Toure.

Dakarun Faransa da sojin Mali sun karbe ikon Birnin Timbuktu bayan karbe ikon birnin Gao manyan biranen Arewacin Mali da ke karkashin ikon Mayakan ansar Dine. Dubban Mutanen Timbuktu ne suka fito suna murna bayan kakkabe ‘Yan tawaye.

Yanzu haka shugabannin kasashen Duniya sun bude Taron Tallafawa Mali a Addis Ababa domin kawo karshen rikicin kasar.

Tuni Kasar Japan ta ce za ta bayar da Dala Miliyan Dari da Ashirin don yaki da 'Yan ta’adda a Yankin Sahel kwanaki goma bayan an kashe mutanenta Goma a Algeria.

Ministan harkokin wajen kasar, Fumio Kashida ya ce kudaden, wani taimako ne don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Mali da kuma Yankin Arewacin Afrika.

Tallafin Japan kuma na zuwa ne bayan Hukumar bayar da Lamuni ta IMF ta amince ta ba kasar Mali rancen kudi Dala Dubu Goma sha Takwas.

Dakarun Faransa kimanin 2,900 ne ke yaki yanzu haka a Mali

Nan gaba kuma ana sa ran Dakarun kasashen Afrika 8,000 da dakarun Chadi za su ci gaba da yaki a Mali. Kodayake ana samun tsaiku har yanzu wajen aikawa da dakarun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.