Isa ga babban shafi

Dakarun ECOWAS suna nazarin yadda za su fara yaki a Mali

Kwamandojin Rundunar Sojin kasashen Afrika ta Yamma suna ci gaba da gudanar da taro a birnin Bamako, don nazarin halin da ake ciki a Mali, da kuma matakan da suka dace a dauka wajen kai daukin Soji.Dakarun Faransa kuma suna nazarin fara yaki ta kasa bayan kwashe kwanaki Biyar suna ruwan wuta ta sama a Arewacin Mali.

Tawagar Tankokin Yakin Faransa akan hanyarsu zuwa Arewacin Mali daga Bamako
Tawagar Tankokin Yakin Faransa akan hanyarsu zuwa Arewacin Mali daga Bamako AFP PHOTO /ERIC FEFERBERG
Talla

Kungiyar ECOWAS tana kokarin gaggauta shirin aika dakarunta domin bin sahun Dakarun Faransa da tuni suka kaddamar da yaki a Arewacin Mali.

Najeriya da ke shirin aikawa da Dakarunta 900 nan da sa’o’I 24, Kwamandan da zai jagoranci dakarun Manjo Janar Umar Shehu Abdulkadir ya shaidawa RFI cewa akwai bukatar su gaggauta shirin da suke yi domin karbe Arewacin Mali daga Mayakan Ansar Dine.

Kanal Mohammed Yarima yace Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayar da umurnin fara tafiya da dakarun nan da sa’o’I 24.

Rahotanni daga Mali sun ce Tankokin yakin Faransa sun isa Yankin Arewaci daga birnin Bamako.

Bayan kwashe kwanaki Biyar ana ruwan wuta ta sama kan ‘Yan Tawayen kasar Mali, yau ake saran dakarun kasar Faransa za su fara yakin kasa, don kwato garuruwan da 'Yan Tawayen suka kama.

Rahotanni daga Bamako sun ce, an ga daruruwan dakarun Mali da na Faransa cikin tankunan yaki sun kama hanyar Diabaly, da ke da nisan kilomita 400 a Arewacin kasar.

Wasu bayanai sun ce, jiragen saman yakin Faransa sun yi ta ruwan wuta a garin na Diabaly daren jiya, a dai dai lokacin da shugaban kasar Faransa, Francois Holland ke cewa, za su kara yawan dakarunsu daga 750 zuwa 2,500 don kakkabe ‘Yan tawayen cikin gaggawa.

Gwamnatin Faransa dai na ci gaba da samun goyon baya daga kasashen Duniya game da yakin da ta kaddamar domin karbe ikon Yankin Arewacin Mali.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin Bil’adama sun yi kiran kiyaye rayukan fararen hula a rikicin na Mali. Kamar yadda masana ke bayyana fargabar samun kwararar makamai da ‘yan gudun hijira daga Arewacin kasar zuwa kasashen da ke makwabtaka da Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.