Amnesty ta nemi a kiyaye rayuwar fararen hula a Mali
Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International ta yi gargadin bangarorin da ke yaki a kasar Mali su tabbatar da sun kiyaye rayukan fararen hula da ke kasar a wata sanarwa da Kungiyar ta fitar sakamakon fara kai hare-hare ta sama da sojan kasar Faransa suka kaddamar a yankunan Arewacin kasar.
Wallafawa ranar:
Kungiyar Amnesty tace akwai matukar damuwa game da halin da fararen hula za su shiga sakamakon rikicin Mali.
A cewar Paule Rigaud Darektan kungiyar mai kula da Nahiyar Afrika ba su fidda tsammanin za’a abkawa wadanda ba su san hawa ba ba su san sauka ba. Saboda haka suke neman a kiyaye.
Kungiyar tace tana da hakkin ganin babu wani muzgunawa da aka yi wa Bil’adama, kuma tana bukatar duniya ta mara masu baya domin a tura masu sa ido zuwa yankunan da ake rikicin domin ganin ba a wuce gona da iri ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu