Isa ga babban shafi
Mali-Faransa-MDD

Faransa ta samu goyon bayan Majalisar dunkin Duniya a Rikicin Mali

Gwamnatin kasar Faransa ta samu goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya a hare haren da ta kaddamar domin karbe ikon Arewacin Mali daga hannun ‘Yan tawaye. Shugaba Hollande yace dakarun Faransa 750 ne aka aika zuwa Mali domin yaki da Mayakan Ansar Dine.

Dakarun Faransa a Birnin Bamako kasar Mali
Dakarun Faransa a Birnin Bamako kasar Mali REUTERS/Joe Penney
Talla

Bayan gudanar da taron gaggawa, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana goyon bayansa ga kudirin Faransa.

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da Mutane 30,000 ne suka kauracewa yankin da dakarun Faransa ke luguden wuta tare da zargin ‘Yan tawayen suna haramtawa mutane zuwa yankin Kudanci.

Rahotanni sun ce ‘Yan Tawayen Mali sun samu nasarar kwace Diabaly, duk da ruwan wuta ta sama da sojojin Faransa ke yi a sansaninsu da ke Arewacin kasar.

Rahotanni na cewa ‘Yan Tawayen sun yi barazanar kai hari tsakiyar Faransa, yayin da jiragen saman yaki ke ci gaba da ruwan wuta a garin Douentza, da ke nisan kilomita 800 daga Bamako.

An kwashe tsawon watanni 10 Yankin Arewaci yana karkashin ikon Mayakan Ansar Dine wadanda ke neman tabbatar da shari’ar Musulunci a kasar Mali.

Mazauna birnin Timbuktu sun ce Mayakan sun fice saboda tunanin za’a kai masu hari. Kamar suka fice daga Birnin Gao.

Sai dai kakakin Mayakan na Ansar Dine Senda Ould Boumama yace sun fice ne domin dubarun Yaki tare da kuacewa kisan fararen hula.

Shugaban Kungiyar Jihadi ta MUJAO Abou Dardar, yace za su dauki Fansa domin Faransa tana yaki ne da Musulunci.

Akwai dai Tankokin yaki sama da 30 da Rahotanni suka ce sun keta kasar Cote d’Ivoire zuwa Mali.

Yanzu haka kuma Faransa da Majalisar Dinkin Duniya sun ce za su gaggauta shirya Dakarun Afrika 3,000 zuwa kasar Mali.

Najeriya da za ta jagorancin Dakarun, tace kafin karshen mako za ta aika da dakarunta 600 kamar yadda Shugaba Goodluck Jonatan yace kasashen Ghana da Nijar da Senegal da Burkina Faso da Togo sun yi alkawalin bayar da gudunmuwar Dakarunsu.

Masana dai suna ganin rikicin Mali zai haifar da matsaloli ga kasashen da ke makwabtaka da kasar musamman wajen kawararar makamai da ‘Yan gudun Hijira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.