Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

Kasar Faransa za ta ninka adadin Dakarunta a kasar Mali

Kasar Faransa, ta yi kudurin ninka adadin Dakarunta da ta tura kasar Mali zuwa 2, 500, wannan labarin ya fito ne daga wata majiyar jami’an tsaro da ta tabbatar da wannan yunkurin da kasar ta Faransa ke yi.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande kenan yake jawabi ga Dakarun kasar Faransa
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande kenan yake jawabi ga Dakarun kasar Faransa Reuters/Joel Saget
Talla

Kwakkwarar majiyar jami’an tsaro ta bayyana cewar kasar Faransa na shirin yin hakan ne a hankali ba wai a lokaci daya ba.

Dama dai shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana cewar yanzu haka akwai dakarun kasar Faransa 750 a kasar Mali, amma kuma adadin zai ci gaba da karuwa.

Matakin ninka adadin Dakarun zuwa 2, 500 ya biyo bayan shawarwarin da Ministocin gwamnatin Faransa suka gabatar akan samar da cikakkiyar kariya ga Bamako babban birnin kasar.

Jaridun Faransa sun ruwaito cewar Faransa na shirin aika Dakarunta na wuccin gadi a Mopti da ke a tsakiyar kasar ta Mali, inda daga can ake sa ran za su soma kaddamar da fada a Arewacin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.