Congo ta nemi a kakubawa Rwanda da Uganda takunkumi
Kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya kakabawa gwamnatocin kasashen Rwanda da Uganda takunkumi, saboda yadda suke taimakawa ‘Yan Tawayen kungiyar M 23 bayan fitar da wani Rahoton Majalisar game da rikicin Congo
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ministan sadarwar kasar, Lambert Mende, yace ya dace a sanya takunkumi kan duk wadanda sunayensu sunayensu sukafito a rahotan Majalisar Dinkin Duniya. Yana mai cewa sun san akwai mutane da dama wadanda ke ruwa da tsaki a rikicin Congo.
Tuni dai Kakakin rundunar sojin Uganda, Felix Kulayige, ya yi watsi da rahoton.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu