Isa ga babban shafi
Ghana

Clinton ta kai Ziyara Ghana domin Jana’izar Atta Mills

Sakatariyar harakokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta kai ziyara kasar Ghana domin halartar Jan’izar Marigayi shugaba John Atta Mills wanda za’a binne a yau Juma’a. Ana sa ran halartar wasu shugabannin kasashen Waje a Jana’izar tsohon Shugaban.

Al'ummar Kasar Ghana sun yi jerin gwano domin Halartar Jana'izar Marigari john Atta Mills
Al'ummar Kasar Ghana sun yi jerin gwano domin Halartar Jana'izar Marigari john Atta Mills REUTERS/Yaw Bibini
Talla

Mills ya mutu ne a ranar 24 ga Watan Juli, watanni biyar a gudanar da zabe a kasar Ghana. Bayan mutuwar shi ne aka nada mataimakin shi John Dramani Mahama, a matsayin sabon shugaban kasa.

Ana sa ran Clinton za ta gana da John Dramani Mahama, domin tattauna batutuwan da suka shafi hulda tsakanin Amurka da Ghana da kuma ci gaban Demokradiya a kasar.

Ana sa ran Clinton za ta kai ziyara kasar Benin daga Ghana bayan ta kai ziyara Senegal da Uganda da Kudancin Sudan da Kenya da Malawi da Afrika ta Kudu da kuma Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.