Isa ga babban shafi
Sudan-Amurka

Clinton ta kai ziyara kudancin Sudan

Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton ta fara ziyara kasar Sudan ta Kudu, a wata ziyarar farko da wani babban jami’in Amurka ya kai tun ballewar Juba daga Sudan a bara.Ana sa ran Clinton za ta gana da Shugaba Salva Kiir, domin tattauna rikicin Juba da Arewacin Sudan.

Sakatariyar Harkokin Wajen Kasar Amurka, Hillary Clinton, a lokacin da take zantawa da manema labarai a Uganda
Sakatariyar Harkokin Wajen Kasar Amurka, Hillary Clinton, a lokacin da take zantawa da manema labarai a Uganda
Talla

Tun ballekwar yankin Kudanci a watan Yulin bara, Akwai yarjejeniyar mallakar yankunan da ke da arzikin Man Fetir da har yanzu ake takaddama akai tsakanin Juba da Sudan.

A ranar 2 ga watan Agusta ne wa’adin da Majalisar Dinkin Duniya taba kasashen domin sasanta kansu ya kawo karshe.

A yau Juma’a ne kuma ake sa ran tawagar kasashen Biyu za su gana da wakilan kungiyar tarayyar Afrika da kuma Majalisar Dinkin Duniya don warware rikicinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.