Najeriya
Clinton ta yi kiran aiwatar da sabbin sauye sauye a Najeriya
Sakatariyar Harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta bukaci shugabanin Najeriya aiwatar da sabbin sauye sauyen da za su fitar da al’ummar kasar daga matsanancin talauci, abinda tace shi ya haifar da matsalar tsaron da ya addabi kasar yanzu haka.
Wallafawa ranar:
Talla
Bayan ganawa da shugaba Goodluck Jonathan, da kuma hafsoshin tsaro, Clinton tace Najeriya tana da hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasa da dama, amma hakan ba zai samu ba, sai an samarwa daukacin ‘Yan kasar madafa, kuma an yi yaki da talaucin da ya addabi al’umma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu