Isa ga babban shafi
Najeriya

Kiristoci ba zasu mayar da martani ba, amma Gwamnatin Najeriya tace zata sake tattaunawa da Boko Haram

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Namadi Sambo, ya yi kiran Kungiyar Boko Haram ta fito domin amincewa da tattaunawa don samun zaman lafiya a Najeriya, bayan wasu ‘Yan bindiga sun bindige mutane 20 a wajen Ibadar al’ummar Kirista a Jami’ar Bayero a Kano. Amma bayan kai harin Shugaban Kiristocin Jahar Kano Mista Ransom Bello, yace sun la’anci harin amma ba zasu mayar da martani ba.

lokacin da ake kokarin saka gawawwakin wadanda suka mutu a cikin Mota da kuma wadanda suka samu rauni a harin Jami'ar Bayero a Kano
lokacin da ake kokarin saka gawawwakin wadanda suka mutu a cikin Mota da kuma wadanda suka samu rauni a harin Jami'ar Bayero a Kano REUTERS/Stringer
Talla

03:00

Kakakin Jami’ar Bayaro a Kano, Mustafa Zaharadden

Salissou Hamissou

A jiya Lahadi ne ‘Yan Bindiga dauke da bama bamai da bindigogi suka kashe mutane 20 bayan bude wuta a wajen Ibadar Kirista a Jami’ar Bayero a Kano.

Shaidun gani da ido sun ce an ji karar harbe harbe da bindiga, da fashewar wani abu da ake kyautata zaton bom ne.

Shaidun sun ce maharan sun isa inda ake gudanar da ibadan ne akan mota da babura, inda suka bude wuta.

Amma Mustafa Zahradeen, Jami’in hulda da Jama’a na Jami’ar Bayero ya shaida wa Rfi cewa mutane Bakwai ne suka rasa rayukansu.

Har yanzu babu wata kungiyar da ta fito ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin, sai dai ana zargin ‘yayan kungiyar Boko Haram ne saboda hare haren da suke kai wa a wuraren ibadar Mabiya addinin Kirista.

00:27

Kalaman Namadi Sambo Mataimakin Shugaban Najeriya

Shehu Saulawa

A jiya Lahadi a Birnin Maiduguri an sake samun mutuwar mutane Hudu bayan kai hari a wani wajen ibadar mabiya addinin Kirista.

Kungiyar Boko Haram ta fito Fili ta dauki alhakin kai harin ranar 20 ga Watan Janairu, hari mafi muni da aka kai a Jahar Kano wanda da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 185.

A ranar Alhamis wasu jerin bama bamai sun tashi a ginin Ofishin Jaridar This Day a Biranen Abuja da Kaduna kuma mutane akalla 9 ne suka mutu.

A lokacin da ya kai Ziyara ginin Ofishin Jaridar This Day , Shugaba Goodluck Jonathan bai amsa ko akwai sake yunkurin tattaunawa da Kungiyar Boko Haram ba.

03:25

Rahoton Shehu Saulawa

Shehu Saulawa

Amma mataimakinsa a wata Ziyara da ya kai Birnin Gombe, Alhaji Namadi Sambo ya nemi kungiyar Boko Haram su fito domin tattaunawa don kawo karshen jubar da jini a kasar.

Sau biyu ne dai kungiyar Boko Haram ke aiko da Sakon gargadin karya gwamnatin Goodluck Jonathan ta Intanet tare da gargadin kai hare hare ga makiyan addinin Islama.

Yanzu haka Jami’an tsaron sun ce suna gudanar da bincike domin gano wadanda suka kai hari a Jami’ar Bayero a Kano.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.