Isa ga babban shafi
Libya-Nato

Kungiyar Amnesty ta bukaci NATO ta binciki hallaka fararen hulan Libya

Kungiyar Amnesty International ta ce dole kungiyar kawancen Tsaro ta NATO, ta binciki yadda dakarun ta suka kashe fararen hula a yakin da ta yi a kasar Libya, da kuma biyan diyya ga iyalan da abin ya shafa.Wani rahoto da kungiyar ta Amnesty International ta fitar yau Litini, ya ce kungiyar ta samu bayanai kan fararen hula 55 da aka kashe, cikinsu harda yara 16, da mata 14, a harin sama da NATO ta kai garuruwan Tripoli, Aliten, Majer, Sirte da Brega. 

Reuters
Talla

Harin da kungiyar NATO ta kai Libya wanda ya kauda da Tsohon shugaban kasa Marigayi Muammar Gaddafi daga mulki, ya haifar da rashin jituwa a tsakanin wakilan kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar Amnesty ta amince da kokarin da NATO ta yi wajen kauce kai hari kan fararen hula, amma ta koka kan kin bincika korafin da aka yi na kashe wasu fararen hular.

Kungiyar ta bukaci NATO ta gudanar da binciken gaggawa dan hukunta jami’an da suka karya dokar duniya, wajen kashe fararen hula, a harin sama da aka yi ta kaiwa kan gidajen jama’a.

Tuni dai kasashen Rasha, China, Afrika ta kudu da Indiya suka zargi NATO da sabawa yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.