Isa ga babban shafi
Libya

Wani Kwamitin kasar Libya ya gano kabari dauke gawauwaki 163

Kwamitin da aka kafa dan gano mutanen da suka bata a Libya, ya ce sun gano wani kabari mai dauke da mutane 163, wadanda aka kashe, lokacin yakin kauda Tsohon shugaban kasa Marigayi Muammar Gaddafi.Wakilin kwamitin, Maher Warfalli, ya bayyana gano gawawaki 163 daga cikin mutane 400 da aka ce sun bata a matsayin abin bakin ciki. 

Reuters/Esam Al-Fetori
Talla

Hukumomin kasar ta Libya sun nemi gafara kan yadda wasu 'yan bindiga suka tone kaburburan sojojin Birtaniya da Italia da suka yi yakin duniya na biyu, a kasar.

Gwamnatin kasar ta ce, halin 'yan bindiga ya yi hannun riga da halin Islama.

Ministan kula da harkokin wajen Britaniya, Jeremy Browne, ya bayyana bacin ransu akai,
bayan ganin hotunan cin zarafin kaburburan yaki a kasar Libya, amma ya nemi gwamnatin Libya ta magance matsalar da aka samu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.