Isa ga babban shafi
Libya

Majalisar Rikon Libya ta sake zaben shugabanta

Majalisar Rikon kwaryar kasar Libya, ta sake zaben Mustafa Abdel Jalil a matsayin shugaban ta, kana kuma an sama masa maitaka guda biyu, da suka hada da Mustafa al Harun, da Salim Qanan.

Mustafa Abdel Jalil shugaban rikon kasar Libya
Mustafa Abdel Jalil shugaban rikon kasar Libya REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Wani jami’in Majalisar, Mustafa Landey, ya ce shugabanin zasu rike mukamin nasu, har sai an gudanar da zabe a watan Yuni mai zuwa. An kafa majalisar rikon yayin juyin juya halin kasar da ya yi sanadiyar kawar da gwamnatin Marigayi Shugaba Muammar Gaddafi cikin shekarar data gabata ta 2011.

Yanzu kasar ta Libya tana fuskantar kalubalen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalia tare da kwace makamai daga hanun tsaffin baraden da suka yi yakin kawar da gwamnatin Gaddafi ta shekaru 42.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.