Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi tir da hari da bam na garin Jos

Harin da aka kai kan wata mujami’a dake garin Jos,ya yi sanadiyar hallaka mutane uku, yayin da wasu fiye da 30 suka samu raunika.Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da harin, ta hannun kakakin sa Reuben Abati. 

REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

03:54

JOS SUNDAY CHURCH BOMB BLAST-edited

A Jihar Bauchi 'yan sanda sun tabbatar da kama mutane takwas, dukkaninsu Kiristoci, wadanda suka yi yunkurin tayar da bam cikin wata mujami'a a kauyen Miya Barkatai cikin karamar hukumar Toro dake cikin jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Ikechukwu Aduba, ya ce jami'an tsaro sun zabura cikin hanzari wajen takawa maharan burki.

Rohotanni sun ce mutanen da suka yi yunkurin tayar da bam din, masu adawa da shuhabanci cikin wannan mujami'a ce.

Hukumomin Jihar Gombe, sun rage lokacin dokar hana fita, daga sa’oi 24, zuwa 13, inda dokar zata fara aiki daga karfe 5 na yamma, zuwa 6 na safe, yayin da Gwamnan Jihar, Ibrahim Dankwambo ya jajantawa mutanen da rikicin ya shafa. Hari 'yan bindiga da suka yi yunkurin fasa gidan yarin jihar ya janyo mutuwan mutane 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.