Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan Bindiga sun yi yunkuri fasa gidan fursuna a Najeriya

Rohotanni daga garin Gombe fadar gwamnatin Jihar Gombe da ke Tarayyar Najeriya sun tabbatar da mutuwan mutane 12, yayin da ‘yan bindiga suka yi yunkurin fasa gidan fursuna.

Reuters/Stringer
Talla

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Gandi Ebikeme Orubebe ya shaida wa manema labarai cewa jami’an tsaro sun mayar da martani tare da cin karfi maharan bayan kwashe sa’oi biyu ana musanyen wuta tare da amfani da bababe masu fashewa daga tsagerun.

Akwai ‘yan sanda biyu da suke cikin wadanda suka rasa ransu, soja daya ya samu raunika, sauran mutane 10 akasari maharan suka hallaka.

A wani labarin, wasu maharan sun hallaka mutane biyar a Masallaci da ke garin Kano birni mafi girma da ke yankin Arewacin Tarayyar ta Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.