Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Shugaban Zimbabwe Mugabe ya yi bikin cika shekaru 88

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, daya daga cikin shugabannin da su ka fi kowane Shugaba a Afrika dadewa a mulki, ya ce yana nan daram yana iya tsayawa takaran zaben kasar.

Talla

Shugaban na wadannan kalamai ne yau Talata, a Harare babban birnin kasar cikin bikin cika shekaru 88 da haihuwa.

Shugaba Mugabe ya ce yana nan tangaran, amma bai fidda tsammanin nan gaba yana iya kamuwa da rashin lafiya ba.

Shugaban wanda ya ke maida martani game da wasu kalamai da ke cewa yana fama da rashin lafiya, ya ce karya ake masa, ya na ji kamar yau aka haife shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.