Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mugabe zai yi bukin cika shekaru 88 na haihuwa

Shugaban Kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, zai yi bukin cika shekaru 88 a duniya, kwanaki bayan sake tsayar da shi a matsayin Dan takaran shugaban kasa. Mugabe shi ne Shugaban da ya fi dadewa saman karagar mulki a Afrika.

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Talla

Shugaban ya yi watsi da jitar jitar rashin lafiyarsa, a cewar Mugabe, akwai lokacin da zai kwanta rashin Lafiya amma yanzu yana jin kansa ne kamar dan shekaru 18.

Tun a shekarar 1980 Mugabe ke shugabanci a kasar Zimbabwe amma yace zai sake tsayawa takara a zaben da yake neman a gudanar a bana sabanin kudirin Fira ministan kasar Morgan Tsvangirai wanda ya nemi sake fasalta kundin tsarin mulki karkashi yarjejeniyar gwamnatin karba-karba.

A watan Disemba ne Jam’iyyar Zanu PF ta tsayar da Mugabe a matsayin dan takararta.

A ranar Assabar ne za’a gudanar da wani gangami domin taya shugaban murnar cika shekaru 88 tare da kaddamar da yakin neman zabensa a birnin Mutare.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.