Isa ga babban shafi
Najeriya

Kimanin mutane 30 sun mutu a Maiduguri

Mutane kusan 30 sun mutu a birnin Maiduguri na Jahar Borno a Tarayyar Najeriya bayan da wasu ‘Yan bindiga da ake zargin ‘Yan boko Haram ne suka bude wuta tare da dala bom a kasuwar Baga reshen masu sayar da Kifi.

Wani harin Bom daya tashi a kasuwar Gomborun Gala a Jahar Borno
Wani harin Bom daya tashi a kasuwar Gomborun Gala a Jahar Borno REUTERS/Stringer
Talla

Kakakin Rundunar Sojin Jahar Kanal Hassan Muhammad ya tabbatar da faruwar al’amarin amma ya musanta samun mutuwar fararen hula inda yace jami’an tsaro sun kashe ‘Yan bindigar guda Takwas a musayar albarussai.

Wata Jami’ar kiyon Lafiya a Maiduguri ta shaidawa kamfanin Dillacin labaran Faransa AFP cewa akwai mata da kananan Yara cikin wadanda suka mutu.

Kanal Hassan yace misalin karfe 1:30 na rana ne a jiya Litinin ‘Yan bindigar suka bude wuta a kasuwar Baga.

Shaidun gani da ido a kasuwar sun ce ‘Yan bindigar sun dala Bom kimanin Takwas da ya tarwatsa kasuwar.

‘Yan bindigar dai suna zargin ‘Yan kasuwar ne wajen ba Jami’an tsaron hadin kai da aka cafke wasu da ake zargin ‘Yan kungiyar Boko Haram ne dake buya a kasuwar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.