Isa ga babban shafi
Mali-Nijar-Burkina

Daruruwan mutane suke gudun hijira daga Mali

Akalla ‘Yan gudun hijira 35,000 suka tsere daga kasar Mali zuwa kasashen Burkina Faso da Nijar, don samun mafaka sanadiyar rikicin da ake ci gaba da gudanarwa tsakanin ‘Yan tawayen Tuareg da dakarun Gwamnati.

Wasu 'Yan gudun Hijira da ke kaura daga kasar Somalia sanadiyar rikicin gwamnati da kungiyar Al shabab
Wasu 'Yan gudun Hijira da ke kaura daga kasar Somalia sanadiyar rikicin gwamnati da kungiyar Al shabab Reuters/Feisal Omar
Talla

Ministan kudin Nijar, Mahmadou Ouhoumadu ya shaida wa manema labarai cewa ‘Yan gudun hijira sama da 23,000 ne suka gudu zuwa Nijar daga Mali.

Ministan yankunan kasar Burkina Faso yace sama da mutane 12,000 ne suka tsallaka zuwa kasar daga Mali.

Hukumar agaji ta Red Cross tace akalla mutane 60,000 suka shiga cikin wani hali sanadiyar rikicin da ake yi a kasar Mali.

Hukumar ‘Yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane 44,000 suka tsallaka zuwa kasashen Burkina Faso da Nijar da Mauritania.

A makon jiya Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty international ta danganta rikicin kasar Mali a matsayin rikici mafi muni cikin shekaru Ashirin da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.