Isa ga babban shafi
Tunisia

An zabi Marzouki, tsohon madugun adawa a matsayin shugaban kasar Tunisia

Majalisar Kasar Tunisia, ta zabi tsohon shugaban ‘Yan adawar kasar, Moncef Marzouki, a matsayin sabon shugaban kasa, wata guda da rabi bayan zaben ‘Yan Majalisun kasar, wanda ya biyo bayan juyin juya hali kifar da gwamnatin Zainul Abidina bin Ali.

Sabon Shugaban Tunisia Moncef Marzouki
Sabon Shugaban Tunisia Moncef Marzouki AFP
Talla

Marzouki da ke jagorancin Jam’iyar Congress for the Republic Party, ya samu kuri’u 153 daga cikin 217 dake Majalisar.

A watan Janairu ne al’ummar Tunisia suka kifar da gwamnatin Zainul Abidina Bin Ali shugaban da ya kwashe shekaru yana shugabancin kasar. A watan Octoba ne kuma aka gudanar da zaben ‘Yan Majalisu domin rubuta sabon kundin tsarin mulki tare da kafa gwamnatin riko.

Ana sa ran Marzouki zai zabi sabon Fira Minista daga Jam’iyyar Musulunci ta Ennahda Jam’iyyar da ta samu gagarumin rinjaye a majalisar kasar.

Dan shekaru 66 da haihuwa daga jam’iyyar CRP da ke kawance cikin majalisar , ya samu yawan kuri’u 153 daga cikin majalisar mai wakilai 217, inda biyu a majalisar suka kada kuri‘ar kin amincewa, biyu suka yi rowar kuri’un, sauran 'Yan majalisar kuma suka kauracewa zaman majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.