Isa ga babban shafi
Libya

Tawagar motoci ta ratsa Nijar ana sa ran Ghaddafi ne

Wata tawagar motocin sojin Libya ta ratso ta Jamhuriyyar Nijar tare da wasu motocin alfarma da dama inda suka kama hanyar Niamey babban birnin kasar, kuma ana zaton Shugaban Libya ne Muammar Gaddafi.Tawagar motocin da suka tasamma kusan 200 zuwa 250 rehotanni na cewa tawagar ta samu kariya ne daga Sojin Nijar. Wata Majiya daga sojin Faransa tace tawagar Shugaba Gaddafi ce akan hanyarsa zuwa kasar Burkina Faso wacce ta yi masa tayin mafaka.Kasar Faransa dai ta taka muhimmiyar rawa a rikicin Libya, akan haka ne ake tunanin tawagar ta samu yardar kungiyar kawancen NATO kafin samun damar tsallakewa daga Libya.Wata Majiya ta shaidawa kamfanin dillacin labaran AFP cewa kasar Faransa ce ta shiga tsakanin sabuwar Gwamnatin ‘yan Tawaye da shugaba Gaddafi.Sai dai kuma har yanzu gwamnatin Faransa bata bada tabbacin rehoton Tawagar ta Libya da ta ratso cikin arewacin Nijar zuwa birnin Agadaz. 

wata motar yakin Libya masu adawa da Gaddafi
wata motar yakin Libya masu adawa da Gaddafi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.