Isa ga babban shafi
MDD-Libya

MDD tace zata taimakawa zaben Libya

Majalisar Dunkin Duniya tace a shirye ta ke ta taimakawa gwamnatin ‘Yan Tawayen Libya a shirye shiryensu na gudanar da zabe a cikin kasar.A cewar Jekadan Majalisar Dunkin Duniya a Tripoli Ian Martin, a jerin bukatun da ‘Yan Tawayen suka fi ba muhimmaci domin tallafa masu shi ne shirya gudanar da zabe.Tun a karshen mako nan ne jekadan Majalisar Dunkin Duniya mai bai wa Ban Ki-moon Shawara ya kai ziyara a Tripoli domin tattaunawa da hukumomin Libya dangane da hanyoyin da suke Tunanin Majalisar Dunkin Duniya zata taimaka masu.  

'Yan kasar Libya mazauna kasar Faransa lokacin da suke gudanar da zanga zangar adawa da Muammar Gaddafi
'Yan kasar Libya mazauna kasar Faransa lokacin da suke gudanar da zanga zangar adawa da Muammar Gaddafi Reuters/Benoît Tessier
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.