Isa ga babban shafi
Libya

Yan Tawayen Libya sun samu nasara kan dakarun Gaddafi

Shugaban Kasar Libya, Muammar Ghadafi, ya ce ya fice daga gidansa, da 'yan tawaye suka kama mamaye, a wani shiri na sake dabara.Shugaban ya ce, ya badda kama inda ya zaga wasu sassan birnin Tripoli, kuma ya tabbatar da cewar, birnin baya cikin mummunar hadari.Yayin da ya ke jawabi a wata tashar radiyo, mallakar Dan sa, Saif al Islam, ya ce babu inda za shi, a Libya zai mutu.Ministan yada labaran sa, Musa Ibrahim, ya ce magoya bayan shugaban 6,500 sun shiga Tripoli babban birnin kasar, kuma zasu basu makamai dan shiga yakin ceto kasar.Gwamnatin Tarayyar Nigeria, ta bukaci sabbin shugabanin Libya, da su kauda banbancin dake tsakanin su, domin hada kan 'yan kasar, dan maida ita tafarkin demokradiya.Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta sanar da haka, inda ta sake jaddada goyan bayan ta, kan kudirin Majalisar Dinkin Duniya, na kauda Gaddafi daga mulki.Anasa bangaren, wani Dan Majalisar Amurka daga Jam’iyar Democrat, Dennis Kuchinich, ya ce dole kungiyar kawancen Tsaro ta NATO ko OTAN, ta dauki alhakin mutuwar fararen hula a Libya.Dan Majalisar ya ce, duk da yake kungiyar na fakewa da kudirin Majalisar Dinkin Duniya, su ma basu fi karfin doka ba.Daga ranar Asabar data gabata da ‘yan tawayen suka kaddamar da yakin karbe birnin Tripoli, kuma tun ranar Asabar sun kwace garin Brega mai dimbin arzikin man fetur, ‘yan tawayen, dake samun goyon bayan Dakarun kungiyar kasashen NATO/OTAN suka fara dannawa don neman shiga birnin Tripoli, inda watanni shida, mayakan Shugaba Gaddafi suka ja daga.Lahadi kuwa ‘Yan tawayen suka ce sun shirya tsaf domin kama garin Tripoli, kuma ta ruwa ‘yan tawayen suka kutsa kai daga yankin Misrata bayan an gabza fada.Shi dai Shugaba Gaddafi yayi jawabai har uku, amma babu wanda zaice ga takamaiman inda yake.Daga inda yake Shugaba Gaddafi ya ce babu gudu babu ja da baya, a fito ayi fada sosai domin kare kasar daga wadanda ya kira beraye da azzalumai.Bayan wani lokaci ne mai Magana da yawun Gwamnatin ya fito ta kafofin labarai ya ce anyi hasarar mutane 1,300 ran Lahadin, kafin ‘yan tawayen su kama wani katafaren fili dake tsakiyar Tripoli, da ake kira Green Square.Da yawa daga cikin mutanen kasar sun yi ta ruguntsumin murnar fara kama birnin na Tripoli ranar Lahadi, har zuwa ranar Littini.‘Yan tawayen sunyi ta mamaye babban birnin kasar ta ruwa, daga Misrata, har dai Dakarun Gaddafi suka ja baya sosai.Daga bisani ne dai Jagoran ‘yan tawayen Mustapha Abdel Jalil, ya furta cewa an kawo karshe Mulkin Gaddafi, kafin Shugabannin kasashen duniya suka rika rige-rigen furta farin cikinsu.Kasar China ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranci sake gina kasar ta Libya, domin samun shugabanci na gari.Ministan harkokin wajen Yang Jiechi, ya yi kuma kira ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, dan yin aiki da kungiyar kasashen Afrika, da kuma ta kasashen Larabawa, domin samun kwanciyar hankali da shugabanci na gari a kasar.

REUTERS/Esam Al-Fetori
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.