Isa ga babban shafi
World-Libya

Taron kasashen kawancen Libya a Paris

Kasashen kawancen Libya sun amince da nasarar ‘Yan Tawayen Libya tare da ci gaba da yaki da Gaddafi gab da bude taron shugabannin kasashen kawancen libya a birnin Paris.Gab da bude taron ne kasar Rasha wacce ada ke adawa da kungiyar NATO, ta bayyana amincewa da gwamnatin ‘Yan Tawaye, bayan da gwamnatin Faransa ta bude asusun bankin Libya na kudi sama da Dala Biliyan biyu.Wata barazana da ke kunnu kai tsakanin kasashen ita ce gargadin da Saiful Islam ya yi na cewa zasu ci gaba da yaki ba kyaf-kyaftawa.Kasar Faransa wacce ke jagorancin taron ta bayyana matukar farin cikinta bayan da kasar Algeriya ta bayyana cewa zata halarci taron tare da amincewa da gwamnatin ‘Yan Tawayen libya. Kasar Africa ta kudu jigo a kungiyar Tarayyar Africa ta kyamaci taron.Taron dai zai samu halartar shugabannin kasashen duniya 60 inda shugabannin zasu tattauna batun kudaden tallafin da zasu bai wa ‘Yan Tawaye tare da tabbatar da huldar Diplomasiya tsakanin kasashen da sabuwar gwamnatin Libya.  

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy tare da jekadun kasashen duniya a taron kasashen kawancen Libya.
Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy tare da jekadun kasashen duniya a taron kasashen kawancen Libya.
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.