Isa ga babban shafi
Nigeria

Mutane 18 sun mutu a Bauchi sanadiyar Cutar Kwalera

Hukumomin Nigeria sun ce mutane 18 sun mutu sanadiyar barkewar annobar kwalera a Jahar Bauchi da ke arewacin kasar. Yanzu haka kuma jami’an kiwon lafiya sun ce cutar ta fara yaduwa a sassan yankunan Bauchi, musamman yankin Gundumar Warji inda mutane 10 suka mutu.Shugaban karamar hukumar Warji Adamu Yahaya ya tabbatar da mutuwar mutane 10 wasu kuma 30 yanzu haka na kwance a gadon asibiti.A Jahar Yobe da Sakkwato kusan mutane 35 ne suka mutu sanadiyar cutar ta kwalera wasu kuma da dama ke kwance a gadon asibiti.  

Masu fama da cutar Kwalera kwance a gadon asibiti
Masu fama da cutar Kwalera kwance a gadon asibiti AFP/ Roberto Schmit
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.