Isa ga babban shafi
Niger

Jumhuriyar Nijar ruwan kogin kwara sun yi barna a Yamai

Bodewar ruwan kogin kwara,ya hadasa barna a birnin Yamai na jumhuriyar Nijar.Alkaluman kididiga sun nuna cewa mutane sama da dubu 5 sun kassance ba su da mahalli sanadiyar lamarin.Tun dai shekara ta 1929,wato kimanin shekaru 81 kenan ba a taba ganin irin wanan ambaliya ba, cewar Abdou Gero kwarare kan harakar yanayi a hukumar da ke kulla da kududubin kogin kwara da ke da cibiyar ta a birnin Yamai.Ekokin noman shinkafa sana da dari 5 ne ambaliyar ruwan ta mamaye.Gwabnan jahar Yamai, Kanal Soumana Djibo ya yi kira ga kungiyoyin masu zaman kansu na kasar da na waje da su kawo gudun muwa ga jama’a.Banar ambaliyar ruwan ,bayan Yamai ta shafi jahohin Tillabery da na Dosso. 

Nijar ambaliyar Ruwan kogin kwara a Birnin Yamai
Nijar ambaliyar Ruwan kogin kwara a Birnin Yamai AFP / Boureima Hama
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.