Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Amurka za ta sake girke soji a gabas ta tsakiya don barazana ga Iran

Kasar Amurka na shirin sake girke wasu karin dakaru dubu guda a yankin gabas ta tsakiya don kara matsin lamba ga Iran, inda ta ke ci gaba da zarginta da hannu a hari kan tankokin man Saudiya na baya-bayan nan, dai dai lokacin da kasashen China da Rasha ke gargadin Amurkan game da tunzura rikicin yankin gabas ta tsakiya.

Shugaban Amurka Donald Trump a tsakiyar wasu dakarun sojin kasar
Shugaban Amurka Donald Trump a tsakiyar wasu dakarun sojin kasar REUTERS
Talla

Matakin na Amurka kan sake girke tarin dakaru a yankin na Gabas ta tsakiya na zuwa ne dai dai lokacin da Iran ta bayar da wa’adin kwanaki 10 ga manyan kasashen duniya wajen ganin sun cimma mata muradanta kan yarjejeniyar nukuliyarta da Amurka ta juyawa baya ko kuma ta dauki matakin fara karya dokokin da yarjejeniyar ta kunsa.

Takaddama tsakanin Iran da Amurka ta tsananta ne tun bayan ficewar Washington daga yarjejeniyar Nukiliyar Tehran baya ga fara girke jami’an tsaronta a yankin gabas ta tsakiya tare kuma da ayyana jami’an tsaron juyin-juya halin Iran din a matsayin tawagar ‘yan ta’adda.

Cikin wata sanarwar da ma’aikatar harkokin tsaron Amurka Pentagon ta fitar, ta ruwaito Patrick Shanahan mukaddashin shugaban ma’aikatar na cewa za su kara yawan dakarunsu da ke yankin gabas ta tsakiya da akalla dakaru dubu 1 galibi sojin ruwa don bayar da cikakken tsaro ga barazanar Iran a yankin.

Cikin jawabansa, Shanahan ya ce bayanan sirrin da ke hannunsu ya nuna yadda Iran ke fadada ta’addancinta ga kasashen yankin tare da hana musu sakat, wanda ya zama wajibi a basu tsaron da su ke bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.