Isa ga babban shafi
WHO

Yaki da safarar taba sigari zai kankama nan da watan Satumba

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da ranar 25 ga watan Satumba mai zuwa a matsayin ranar da dokar hana safarar taba sigari za ta fara aiki, a dai dai lokacin da Birtaniya ta amince da mara mata baya.Birtaniyar dai ita ce kasa ta 40 da ta amince da kudirin na WHO wanda hukumar ta ce hakan babban kwarin gwiwa ne gare ta.

WHO ta ce fiye da mutane miliyan 7 ne ke mutuwa duk shekara sanadiyyar taba sigari, yayin da duniya ke tabka asarar fiye da dala tiriliyan guda da rabi.
WHO ta ce fiye da mutane miliyan 7 ne ke mutuwa duk shekara sanadiyyar taba sigari, yayin da duniya ke tabka asarar fiye da dala tiriliyan guda da rabi. Reuters
Talla

WHO ta ce shigowar Birtaniya da Arewacin Ireland yakin da ta ke da safarar tabar sigari ba bisa ka’ida ba ya kara mata kaimi ganin yadda ta cimma kai wa kasashe 40 wadanda da su ne take bukatar yin aiki da su don tabbatar da hanin.

Hukumar lafiyar ta duniya ta ce nan da kwanaki 90 masu zuwa wanda ya yi dai dai da 25 ga watan Satumba dokar hana safarar tabar sigari za ta fara aiki yayinda za afara hukunta wadanda aka samu da karya dokar a sassan duniya daban daban.

Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom ya ce shigowar Birtaniya yakin da ta ke da safarar taba sigarin babban abin farin ciki ne kuma na ci gaba ga hukumar a yakin da ta jima tana neman goyon bayan kasashe.

Tun a shekarar 2012 hukumar ta WHO ta gabatar da kudirin ga kasashe don ganin sun mara baya a yakin da ta ke da safarar taba sigari, amma kasashen suka gaza daukar batun da muhimmanci.

A cewar Dr Tedros lokaci ya kusa da za a fara daukar mataki kan masu safarar tabar ba bisa ka’ida ba, wanda hakan ya kawo karshen tafiyar hawainiyar da kudurin na su ke fuskanta a manyan kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.