Yau 8 ga watan maris ita ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin mata, inda a kowace shekara rana mai kamar ta yau ake tattauna matsalolin da mata ke fuskanta a sassan duniya.A bana dai, an yi wa ranar take da ‘’Rawar da masu fafutuka ke takawa domin samar da sauyi a rayuwar matar a birane da kauyuka".‘Yar majalisar dattawan Faransa Claudine Lepage, yanzu haka tana ziyara a Najeriya domin gabatar da wata kasida dangane da wannan rana a birnin Lagos, ta kuma bayyana wa Abubakar Issa Dandago sakon da take dauke da shi dangane wannan rana.
Sauran kashi-kashi
-
Munyi mamakin yadda Amurka ta san bayanan sirrin tsaron mu - Raɗɗa
Wasu gwamnonin arewacin Najeriya 10 da ke fuskantar matsalolin tsaro, sun kammala taron da suka je Amurka kan matsalar da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya.26/04/202405:17 -
Bashir Dan-Malam kan karancin man fetur a sassan Najeriya
Rahotanni daga sassan arewacin Najeriya na nuna cewar an fara samun karancin mai a gidajen mai, abinda ya sa wasu masu man suka kara farashin da suke sayar da kowacce lita.25/04/202403:16 -
Arewa maso Yammacin Najeriya ne mafi hatsari saboda matsalar tsaro - Bincike
Kungiyar 'Global Rights' ta bayyana yankin arewa maso yammacin Najeriya a matsayin mafi hadari, saboda yadda 'yan bindiga ke kisa da take hakkin Bil Adama ba tare da kaukautawa ba.18/04/202403:16 -
Kuskure ne a yi tunanin ɗagawar darajar naira ba zai ɗore ba - Dakta Kurfi
Darajar Naira na cigaba da ɗagawa a Najeriya tare da saukar farashin wasu kayayyakin abinci a wasu kasuwannin ƙasar, abinda ya sa wasu tunanin cewar tasirin saukar Dalar ne ya sanya wasu kayayyakin suka fara sauka.17/04/202403:19 -
Tattaunawa da Sanata Ikira Aliyu Bilbis kan tsaro a jihar Zamfara
Hukumomi a Najeriya daga matakin jiha zuwa na kasar baki ɗaya na daukar matakai daban daban wajen samar da zaman lafiya a jihar Zamfara, amma har ya zuwa wannan lokaci ba'a kai ga cimma biyan bukata ba.16/04/202403:26