Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Amurka za ta katse tattaunawar Syria

Kasar Amurka ta yi barazanar katse duk wani hadin-kai da Rasha don warware rikicin Syria sakamakon hare-haren saman da ake ci gaba da kaddamarwa a birnin Aleppo.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov
Talla

A wata hira da ya yi ta wayar tarho da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce, Amurka ta dora wa Rasha laifin amfani da munanan bama-bamai wajen kai hare-haren a birnin Aleppo na Syria.

Mr. Kerry ya ce, matukar Rashan ta ci gaba da kai wanann farmakin, to lallai hakan sai sabbaba yankewar duk wata hulda da ke tsakaninsu ta kawo karshen rikicin na Syria

Tun lokacin da yarjejeniyar tsagaita musayar wutar Syria ta kawo karshe a cikin makon jiya, birnin na Aleppo ya gamu da munanan hare-haren sama, abin da haddasa asarar rayuka, cikin su har da kanana yara.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya yi Allah-wadai da hare-haren, wadanda suka shafi wasu manyan asibitoci guda biyu a yankin da ‘yan adawa ke rike da shi a Aleppo, abin da ya bayyana a matsayin laifukan yaki.

Baya ga asarar rayuka, har ila yau, hare-haren sun yi sanadiyar rushewar gidaje da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.