Isa ga babban shafi
Iraqi

Jami'an tsaro 2000 sun rasa rayukansu a Iraqi

Wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce akalla jami’an tsaro 2,000 suka rasa rayukansu a sassan kasar Iraqi, baya ga daruruwan farraren hula da suka rasa rayukansu a cikin watan Nuwamba da ya gabata.

Wata karamar yarinya da aka ceto a Mosul yayin barin wuta da ake tsakanin sojin Iraqi da mayakan ISIL.
Wata karamar yarinya da aka ceto a Mosul yayin barin wuta da ake tsakanin sojin Iraqi da mayakan ISIL. REUTERS/Khalid al Mousily
Talla

Alkaluman mamatan ya nunka na watan Oktoba a cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya.

Mamatan dubu biyu sun kunshi sojin da suka rasa rayukansu a farmakin kwato birnin Mosul daga hannun mayakan ISIL.

Rahoton ya kuma ce fararren hula fiye da dari tara ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu akalla dari hudu da hamsin suka sami raunuka

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Iraqi Yan Kubis ya ce yawan fararren hular da suka mutu a rikicin abu ne mai tayar da hankali.

An samu asarar rayukan mutane da suka kunshi jami’an tsaro da na farraren hula da dama, tun bayan da dakarun gwamnatin Iraki suka kaddamar da farmakin kwato birnin Mosul daga hannun mayakan ISIL da suka kwace birnin a shekara 2014.

Kawo yanzu dai mayakan ISIL na ci gaba da rike ikon wasu yankuna a Mosul.

A ranar 17 ga watan Oktoba dakarun Iraki suka soma gumurzun kwato birnin na Mosul da ya kasance birni na biyu mafi girma a Iraki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.