Japan zata girke makaman kariyar harin Koriya ta Arewa
Ministan tsaron kasar Japan Naoki Tanaka, ya bada umurni girke makaman kariya daga makamai masu linzami da kasar Koriya ta Arewa zata harba masu cin dogon zango a watan gobe.
Wallafawa ranar:
A Yau Juma’a ne, minista Tanaka ya bayyana wa manema labarai, a Tokyo babban birnin kasar, inda ya ce jiragen ruwan yaki zasu dauk makaman kariyar, da zasu wargaza makamai masu linzamin na kasar koriya ta Arewa.
Cikin watan gobe kasar ta Koriya ta Arewa ta ce zata harba tauraron dan adam sararin samaniya, amma duk wani umurni kakkabo rokar kasar, sai ya samu amincewar Fira ministan kasar ta Japan Yoshihiko Noda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu