Isa ga babban shafi
Japan-China

PM Japan Noda ya gana da shugabannin kasar China

PM kasar Japan Yoshihiko Noda yau Litinin ya gana da Shugabannin China inda yake ziyara, kuma maganar hain da ake ciki a Koriya ta Arewa, bayan mutuwan Shugaba Kim Jong-Il ta mamaye tattaunawar.

Talla

Kasar China ce mafi kusa da Koriya ta Arewa tsakanin kasashen duniya, PM Noda na Japan ya ce samun zaman lafiya cikin wannan yanki shi ne babban abunda yake tattaunawa akai.

Biyu daga cikin sanannun mutane kasar Koriya ta Kudu sun shiga kasar Koriya ta Arewa, domin ta’aziyar shugaban kasar Kim Jong-Il.

Matar Tsohon Shugaban Koriya ta Kudu Lee Hee-Ho da Shugaban Kamfanin Hyundai Hyun Jung-Eun, zasu shafe kwanaki biyu yayin ziyarar. Babu tabbacin zasu gana da sabon Shugaban Kim Jong-Un.

Kasar Koriya ta Kudu ta kare mafi yawan ‘yan kasarta da shiga domin ta’aziyar abunda ya fusata Koriya ta Arewa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.