Isa ga babban shafi
Najeriya

An soma taron kungiyoyin ECOWAS da ECCAS

A yau Litinin ake bude taron kungiyoyin gamayyar tattalin arzikin kasashen yankin Afrika ta yamma wato ECOWAS ko kuma CEDEO, da kuma takwararta ta hadin kan kasashen yankin Afrika ta tsakiya ECCAS a Lome babban birnin Kasar Togo.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin halartar taron ECOWAS kashi na 52, da Najeriya ta karbi bakuncinsa a garin Abuja. 16 ga watan Disamba, 2017.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin halartar taron ECOWAS kashi na 52, da Najeriya ta karbi bakuncinsa a garin Abuja. 16 ga watan Disamba, 2017. FEMI ADESINA
Talla

Taron hadin gwiwar zai mayar da hankali ne kan tattauna yadda kasashen za su hada karfi, wajen yakar ta’addanci, da sauran manyan laifukan da ake aikatawa a tsakanin iyakokin kasashen.

A ranar Talata, 31 ga watan Yuli, shugabannin kasashen yammacin Afrika, karkashin kungiyar ECOWAS za su gudanar da taron shekara shekara, kashi na 53, kan al'amuran da suka shafi yammacin nahiyar ta Afrika.

Daga muhimman batutuwan da taron zai mayar da hankali akai, akwai yanayin siyasa da kuma matsalolin tsaro a kasashen Guinea Bissau, Mali, da mai masaukin baki Togo.

Sauran batutuwan da taron zai tattauna a kai sun hada da rikicin manoma da makiyaya, kwarar ‘yan ci rani daga Afrika zuwa turai da kuma, gudanar da garambawul a tsarin tafiyar da kungiyar ta ECOWAS, domin kara karfin tasirinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.