Isa ga babban shafi
Wasanni

Bama bukatar zaburarwa don lallasa Real Madrid - Guardiola

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce ‘yan wasansa basa bukatar samun kwarin gwiwa daga hukuncin hukumar UEFA da ya haramta musu shiga gasar zakarun Turai tsawon shekaru 2, don lallasa Real Madrid a fafatawar da za su yi a wannan laraba.

Kocin Manchester City Pep Guardiola.
Kocin Manchester City Pep Guardiola. Reuters/Jason Cairnduff
Talla

Sama da mako guda kenan da hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta zartas da hukuncin kan City, bayan samunta da laifin kashe kudade wajen sayen ‘yan wasa sama da adadin kudaden shigar da take samu, zargin da kungiyar ta musanta gami da daukaka kara akai.

A baya bayan nan ne kuma kocin Manchester Cityn Pep Guardiola ya ce yaga shaidun da suka tabbatar da cewa kungiyar bata saba kowace ka’ida ba.

Sau 2 Guardiola na lashe kofin gasar Zakarun Turai a lokacin da ya horasda Barcelona, sai dai bayan komawarsa City, har yanzu bait aba samun nasarar kaiwa ko da zagayen wasan kusa da na karshe; Semi final ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.