Isa ga babban shafi
Wasanni

Conte ya kare kansa daga caccakar masoyan Chelsea

Kocin Chelsea Antonio Conte ya kare matakin tsarin da ya yi amfani da shi a fafatawar da Manchester City ta doke kungiyarsa da ci daya mai ban haushi a gasar firimiyar Ingila a jiya Lahadi.

Kocin Chelsea Antonio Conte
Kocin Chelsea Antonio Conte REUTERS
Talla

‘Yan wasan na Chelsea sun gaza kai kyakkawan harin jefa kwallo a raga ko da sau daya a karawar, yayin da magoya bayansu da masharhanta kan kwallon kafa ke caccakar Conte saboda rashin fara wasan da zaratansa kamar Alvaro Morata da Olivier Giroud, in da ya ajiye su a banci.

Sannan kuma ana ganin cewa, 'yan wasansa sun tare a gida kamar gumaka a cewar, Gary Neville wani kwararren masharhanci a kafar talabijin ta Sky Sport.

Sai dai a cewar Conte, sakarci ne ya fara wasan da wadannan zarata, in da ya bada misali da irin lallasar da Manchester City ta yi wa Arsenal da ci 3-0 har sau biyu a gasar League Cup da firimiya a makon jiya.

Conte ya ce, ba zai yi irin wannan sakaci ba har Manchester City mai jan ragama ta jefa kwallaye uku ko hudu a ragarsa.

Yanzu haka dai, Manchester City ta bada tazarar maki 18 a teburin gasar ta firimiya, abin da ke nuna cewa, babu shakka ta kama hanyar lashe kofin a bana, yayin da ta bai wa Chelsea wadda ke a matsayi na biyar tazarar maki 2.

Bernado Silva ne dai ya jefa kwallon daya tilo a cikin dakika 35 da dawo daga hutun rabin lokaci a wasan na jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.