Isa ga babban shafi
Rasha

Jamus da Chile sun rike juna a Rasha

Jamus da Chile sun rike juna ci 1-1 a karawar da suka yi a jiya alhamis a gasar Gasar cin kofin zakarun nahiyoyin duniya da ake gudanarwa a Rasha.

Jamus da Chile sun rike juna a rukuninsu na B
Jamus da Chile sun rike juna a rukuninsu na B REUTERS
Talla

A wasan ne dan wasan Arsenal Alexis Sanchez ya kafa tarihi a kasarsa ta Chile a matsayin dan wasan da ya fi zirara kwallaye a raga a tarihin kasar bayan kwallon da ya jefa a ragar Jamus.

Chile ce ta fara cin jamus kafin daga bisani Jamus ta farke. Kuma Chile ta kai wa Jamus hare hare da dama.

Sakamakon wasan ya ba Chile damar jagorantar rukuninisu na B da yawan kwallaye tsakaninta da Jamus, inda dukkaninsu ke da maki 4.

A ranar Lahadi ne Jamus zata kara da Kamaru a Sochi, Chile kuma da Australia wacce jamus ta doke 3-2.

Bayan dai kammala wasan a jiya, Sanchez ya ki amsa tambaya kan makomarsa a Arsenal inda har yanzu dan wasan bai sanya hannu kan sabuwar kwangila ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.