Isa ga babban shafi
Rasha-Wasanni

Haramcin shiga wasannin motsa jiki kan Rasha zai cigaba

Bisa dukkan alamu haramcin da aka kakabawa masu wasannin motsa jiki na kasar Rasha a wannan shekara, zai cigaba da wanzuwa har cikin shekara ta 2017, inda za’a yi gasar wasannin motsa jiki ta Duniya a watan Agusta mai zuwa.

Wasu daga cikin 'yan wasan motsa jiki na Rasha da aka tantance kuma suka halarci gasar Olympics da ta gudana a birnin Rio na Brazil
Wasu daga cikin 'yan wasan motsa jiki na Rasha da aka tantance kuma suka halarci gasar Olympics da ta gudana a birnin Rio na Brazil
Talla

Shugaban hukuma mai zaman kanta, da ke sa’ido kan yaki da shan kwayoyin karin kuzari tsakanin ‘yan wasa Rune Andersen, ya shaidawa Majalisar koli ta hukumomin wasannin motsa jiki ta duniya cewa, an samu gyare gyare daga bangaren hukumar kula da wassanin Rasha, sai dai har yanzu akwai sauran ka’idoji da ake bukatar kasar ta cike kafin dage mata haramcin.

Idan ba’a manta ba, yayin da ke dab da fara wasannin Olympics da aka yi a birnin Rio na Brazil, aka bankado yadda wasu ‘yan wasan motsa jiki na Rasha ke amfani da kwayoyin karin kuzari, duk da cewa akwai sanin hukumar wasannin kasar.

A watan Janairu mai zuwa wata tawagar sa’ido zata ziyarci birinin Moscow, don tantance kokarin da hukumar kula da wasannin Rasha dama ‘yan wasan kasar ke yi, na dawo da martaba da kuma yarda tsakaninsu da hukumomin wasanni na Duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.