Isa ga babban shafi
Balon d'Or

Balon d’Or: Ronaldo da Messi na cikin jerin ‘yan wasa 30

An fitar da jerin sunayen ‘yan wasa 30 da za a zabi gwarzon dan wasa a duniya a bana wadanda suka hada Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da suka jima suna lashe kyautar ta Balon d’Or.

Ronaldo da Messi daNeymar na takarar Ballon d'Or
Ronaldo da Messi daNeymar na takarar Ballon d'Or FIFA
Talla

‘Yan wasan Firimiya 8 aka zaba a jerin sunayen 30 da suka hada da Sergio Aguero na Manchester City da Zlatan Ibrahimovic da Paul Pogba na Manchester United da Hugo Lloris na Tottenham Hotspur da Dimitri Payet na West Ham United da kuma ‘Yan wasan Leicester City biyu Riyad Mahrez da Jamie Vardy saboda namijin kokarin da suka yi na jagorantar kungiyar ga nasarar lashe kofin Firimiya a Ingila.

Ronaldo na harin lashe kyautar ne a karo na hudu bayan ya karbi kyautar a 2008 da 2013 da 2014 kuma cikin jerin sunayen akwai abokan wasan shi a Real Madrid da suka hada da Gareth Bale da Luka Modric da Toni Kroos, Sergio Ramos da Pepe.

Ronaldo dai na da fatar lashe kyautar bayan ya lashe kofin zakarun Turai a Real Madrid da kuma taimakawa Portugal lashe kofin Turai a bana.

Messi na harin lashe kyautar a karo na shida, sannan cikin jerin ‘yan wasan 30 akwai abokan wasan shi a Barcelona Andres Iniesta da Neymar da Luis Suarez.

Wata babar Mujallar wasan kwallon kafa a Faransa ce ke daukar nauyin kyautar, kuma a yau litinin ne ta fitar da jerin sunayen.

A can baya dai kyautar ta hadin guiwa ce tsakanin mujallar ta Faransa da kuma hukumar kwallon kafa FIFA.

Amma a bana ne yarjejeniyar ta kawo karshe.

‘Yan jarida ne da Kaftin kaftin na kasashen duniya za su zabi gwarzon dan wasan cikin jerin ‘Yan wasa 30.

Jerin sunayen 'Yan wasa 30.

Sergio Aguero (ARG/Manchester City), Pierre-Emerick Aubameyang (GAB/Borussia Dortmund), Gareth Bale (WAL/Real Madrid), Gianluigi Buffon (ITA/Juventus), Cristiano Ronaldo (POR/Real Madrid), Kevin De Bruyne (BEL/Manchester City), Paulo Dybala (ARG/Juventus), Diego Godin (URU/Atletico Madrid), Antoine Griezmann (FRA/Atletico Madrid), Gonzalo Higuain (ARG/Juventus), Zlatan Ibrahimovic (SWE/Manchester United), Andres Iniesta (ESP/Barcelona), Koke (ESP/Atletico Madrid), Toni Kroos (GER/Real Madrid), Robert Lewandowski (POL/Bayern Munich), Hugo Lloris (FRA/Tottenham Hotspur), Riyad Mahrez (ALG/Leicester City), Lionel Messi (ARG/Barcelona), Luka Modric (CRO/Real Madrid), Thomas Mueller (GER/Bayern Munich), Manuel Neuer (GER/Bayern Munich), Neymar (BRA/Barcelona), Dimitri Payet (FRA/West Ham United), Paul Pogba (FRA/Manchester United), Pepe (POR/Real Madrid), Rui Patricio (POR/Sporting Lisbon), Sergio Ramos (ESP/Real Madrid), Luis Suarez (URU/Barcelona), Jamie Vardy (ENG/Leicester City), Arturo Vidal (CHI/Bayern Munich).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.