Isa ga babban shafi
Tennis

Djokovic da Serena sun lashe Wimbledon

Novak Djokovic ya sake lashe kofin Wimbledon a bana bayan ya doke Roger Federer a wasan karshe da suka fafata a jiya Lahadi. A bangaren Mata Serena Williams ce ta lashe kofin bayan ta doke Garbine Muguruza ta Sifaniya.

Wannan ne kofi na uku da Djokovic ya lashe a Wimbledon cikin shekaru 5.
Wannan ne kofi na uku da Djokovic ya lashe a Wimbledon cikin shekaru 5. REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Djokovic ya lashe kofin ne a dai dai lokacin da ya ke bikin cika shekara da aurensa, inda a bara a rana irin ta jiya ya yi bikin aurensa da Jelena Ristic.

Wannan ne kofi na uku da Djokovic ya lashe a Wimbledon cikin shekaru 5.

Serena Williams ta lashe kofin Wimbledon bayan ta doke Muguruza.

Kofi na shida ke nan da Serena ta lashe a Wimbledon kuma karo na 21 ne da ‘yar wasan ta Amurka ke lashe Grand Slam, manyan gasannin Tennis na duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.