Isa ga babban shafi
Turai

Unal Umery na sa ran lashe kofin Europa Ligue

A yau Chelsea za ta ketse reni da Arsenal a gasar cin kofin Europa Ligue ,wasar da za a yi a filin wasa na Baku dake kasar Azarbeidjan.A cewar manazarta Unal Emery mai horar da kungiyar Arsenal ,zai iya sake shiga tarihi da kafar dama kasancewar ya taba lashe wannan kofi har sau uku da kulob na Sevilla, wanda ake kuma sa ran yin haka zai sake dawo da kungiyar turbar manyan kungiyoyi bayan da ta share kusan shekaru 22 a karkashin jagorancin mai horarsuwa da aka sani da Arsene Wenger.

Unai Emery da wasu daga cikin yan wasan Arsenal Mohamed Elneny, Stephan Lichtsteiner, Granit Xhaka, Henrikh Mkhitaryan
Unai Emery da wasu daga cikin yan wasan Arsenal Mohamed Elneny, Stephan Lichtsteiner, Granit Xhaka, Henrikh Mkhitaryan Reuters/Andrew Boyers
Talla

A daya bangaren a ranar asabar mai kamawa dai akwai karawa da zata hada Liverpool da Tottenham a Madrid dangane da gasar cin kofin zakarun Turai, wanda kuma hakan ke nuna ta yada kungiyoyin kwallon kafar Ingila suka samu ci gaba ,tareda kasance a sahun gaba a batuntuwan da suka jibanci kwallon kafa na Turai a wannan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.