Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta yi hayar mutane don yin bore a Najeriya-Fadar Buhari

Fadar shugaban Najeriya ta zargi babbar jam’iyyar adawa ta PDP da yin hayar mutane kimanin dubu 2 da suka hada da maza da mata domin gudanar da zanga-zangar kyamar manyan hafsoshin tsaron kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Mai magana da yawun fadar shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya ce, wani gungun ‘yan siyasa da ya amfana da rikicin Boko Haram, na biyan kudi ga jama’a domin shiga cikin gagarumar zanga-zangar.

A cikin wata sanarwa mai taken  "siyasartar da tsaro ba zai haifar da alhei ba ga kowa" Shehu ya gargadi 'yan siyasa game da tunzira al'umma don yin bore ga manyan hafsoshin tsaron kasar.

Mai magana da yawun shaguban ya kuma ce, 'yan siyasar za su nemi hadin kan kafofin yada labarai domin cimma manufarsu, abin da ya sa ya bukaci kafofin da sukauce wa daukar bangaranci.

Kazalika fadar shugaba Buhari ta ce, ‘yan adawa ne suka yayata hoton bidiyon da ke nuna yadda aka yi wa shugaban ihu a lokacin ziyarar jaje da yak ai birnin Maiduguri na jihar Borno a ranar Laraba.

Wannan na zuwa ne a daidain lokacin da al'ummar Najeriya ke fatan ganin shugaban kasar ya sauya hafsoshin tsaron kasar saboda suna ganin sun gaza wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa musamman a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da rikicin Boko Haram.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.